(ABNA24.com) Ma’aikatar harkokin wajen Jamus, ce ta fara aiwatar da tsarin na bani gishiri in baka manda, tsakanin kasashen turan da Iran.
A matakin farko kasashen da suka hada da Jamus, Biritaniya da kuma Faransa, sun cimma matsaya ta fara aiki da tsarin ta yadda Iran za ta samu kayayakin asibiti kamar yadda ministan harkokin wajen Jamus ya sanar a shafinsa na Twitter.
Bangarorin sun yi fatan ci gaba da wannan tsarin a tsakaninsu.
A watan Janairu na shekara 2019, ne kasashen turan uku, suka sanar da kafa tsarin mai suna Intex, domin ci gaba da huldar kasuwanci da Iran, amma ba tare da amfani da dalar Amurka.
342